16 Satumba 2021 - 12:59
Shugabannin ECOWAS Za Su Yi Taron Gaggawa Yau Kan Batun Kasar Guinea

A wani lokaci yau Alhamis, ake sa ran shugabannin da gwamnatoci mambobin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, zasuyi wani taro a birnin Accra na kasar Ghana, game da halin da ake ciki a kasar Guinea kwanaki 11 bayan da sojoji sukayi juyin mulki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A makon daya gabata kungiyar ta ECOWAS, ta dakatar da kasar ta Guinea daga zama mamba a cikinta sakamakon juyin mulkin da sojojin sukayi.

A taron nay au, za’a mika wa shugabanin kungiyar rahoton tawagar da ta ziyarci kasar ta Guinea a ranar Juma’a data gabata.

Babbar ayar da ake azawa ita ce ko kungiyar ta ECOWAS, za ta kakaba takunkumi ga kasar ta Guinea, kamar yadda ya wakana kan kasar Mali, yayin juyin mulkin farko da akayi bara.

Kafin hakan dai tawagar ta ECOWAS, da ta ziyarci kasar ta Guinea ta bukaci da a yi mulkin rikon kwarya na fara hula kuma cikin gajeren lokaci, wand aba zai wuce wa’adin shekara guda ba.

Haka kuma ECOWAS, na bukatar da a gaggauta sakin fursunonin siyasa da ake tsare da ciki har da hambararen shugaban kasar Alpha Conde.

A ranar 5 ga watan Satumban nan ne sojoji karkashin jagorancin Kanal Mamady Doumbouya, suka kifar da mulkin shugaba Alpha Conde, wanda ke shugabancin kasar a wa’adi na uku bayan kwaskware kundin tsarin mulkin kasar wanda ya bashi damar sake tsayawa takarar zaben da ya sake lashewa a watan Disamban bara.

342/