16 Satumba 2021 - 12:56
Zimbabwe Za Ta Harba Tauraron Dan Adam Na Farko Mallakin Kanta

Kasar Zimbabwe, ta ce komi ya kallama a shirin da ta ken a harba tauraren da adam na farko mallakin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Za’a har tauraren dan adam din ne mai suna, ZIMSAT-1 a shekarar 2022.

Injiniyoyin Zimbabwe sun ce tauraren ya kai wani mataki na gaba, kuma, ana sa ran kammala duk wasu ayyuka kansa a watan Disamba na 2021.

Za’a kuma kaddamar da shi a Japan a watan Fabrairu na 2022.

ZIMSAT-1 an kera shi karkashin Cibiyar Fasaha ta Kyushu a Japan, kuma Hukumar sararin samaniya ta Japan, (JAXA), ce za ta kaddamar da shi.

Shugaban kasar, ta Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya yaba da aikin, Wanda ya ce babban mataki ne na habaka fasahohin lura da kasa da ci gaban kasa.

Ya bayyana hakan ne, a yayin kaddamar da Hukumar kula da Sararin Samaniya ta Zimbabwe (ZNGSA).

Harba tauraren dan adam din zai baiwa kasar ta Zimbabwe damar sanya ido kan yanayin tafiyar kasa, da sarrafa albarkatun kasa da rage tasirin canjin yanayi.

Haka kuma wannan wani ci gaba ne na shirin kasar na yin mu'amala da sauran kasashe da zama manyan masu fada aji kafin nan da shekarar 2030.

342/