15 Satumba 2021 - 11:32
Iran : Adadin Wadanda Akayi Wa Riga Kafin Korona Na Biyu Ya Kai Kusan Miliyan 38

Hukumomin lafiya a Iran, sun sanar da cewa adadin mutanen da aka riga akayi masu allurar riga kafin korona ta biyu ya kai kusan miliyan 38.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Alkalumman da ma’aikatar lafiya ta kasar ta fitar, sun nuna cewa, ye zuwa ranar Talata mutum miliyan 37 da dubu 866 da dari 551 akayi wa riga kafin na biyu.

Riga kafin da akayi amfani dasu sun hada da Spoutnik, Bharat da Astrazeneca da kuma Barakat.

A baya baya nan dai adadin wadanda akewa riga kafin ya karu matuka a kasar ta Iran.

Samar da riga kafin ga kowa da kowa na daya daga cikin alkawuran da sabuwar gwamnatin kasar ta Iran ta sanya a gaba.

342/