Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ta bayar dea rahoton cewa, a ziyarar da yake gudanarwa yau a birnin Tehran, Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta duniya Rafael Grossi ya bayyana cewa, ya zama wijibi dukanin bangarori na Iran da kuma hukumar IAEA su yi aiki tare da juna.
Wanan ziyara ta zo ne biyo bayan wani rahoto da hukumar ta fitar a makon da ya gabata wanda ya soki irin matakan da Iran take dauka na hana hukumar sanya ido a kan ayyukan nukiliya da kasar ta Iran take gudanarwa, bayan karewar wa’adin da Iran din ta baiwa hukumar.
Ko ranar Alhamis da ta gabata wakilin kasar Rasha a hukumar kula da makashin nukiliya ta duniya Mikhail Ulyanov ya sanar da cewa, kasarsa ba za ta goyi bayan duk wani mataki da hukumar IAEA za ta dauka a kan kasar Iran ba.
Uyanov ya ce babu wani dalili da zai sanya hukumar ta siyasantar da ayyukanta, domin kuwa irin bayannan da ta bayar dangane da shirin Iran na nukiliya a baya-bayan nan ba mu taimakawa ba ne wajen warware takaddamar shirin Iran na nukilya.
A kan haka ya ce, a zaman da alkalan hukumar za su gudanar, idan har suka fitar da wani kudiri na daukar matakan takurawa kasar Iran, to a nan take Rasha za ta yi fatali da shi, kuma za ta hana kudirin wucewa.
342/