Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Gungun jam'iyyun 'yan adawa ne dai suka kawo karshen rinjayen da jam'iyyar take da shi.
‘Yan adawan sun samu ‘yan majalisun dokoki 395, a yayin da jam'iyyar PJD ta samu kujeru 12 kawai.
Wanan dai ya kawo karshen mafarkin jam’iyyar na samun karin wa'adi na uku a kan madafan iko.
A yanzu dai Sarki Mohammed na VI na Morocco ne ke da hurumin nada daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyun da suka yi rinjaye a matsayin sabon shugaban gwamnati.
342/