Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) - ABNA ya bayar, a wani yunkuri mai ban al'ajabi karamar hukumar "lardin Sindh" ta shigar da kara kan masu juyayin Hussaini!
Hujjatul Islam Wal Muslimen "Maqsud Ali Dumaki", babban mai magana da yawun Majalisar Hadin Kan Musulmai ta Pakistan, yayi kakkausar suka kan matakin tsattsauran ra’ayin da karamar hukumar "Sindh" ta dauka kan masu makokin.
Ya bayyana cewa Sayyidus Sajidin Imam Ali Zaynul Abedin (AS) da Sayyida Zainab AlKubra (AS) ba wai kawai sun kare manufofin shahadar dan Annabi Imam Husaini (AS) ba ne, har ma yan kunshi fadakar da Mutanan Duniya gaba daya kan manufofi da makasudin shahada tare da bayyana cin hanci da rashawa na batacciyar gwamnati Hukumar Umayyawa da mayar da bukin samun nasarar mulkin Yazid a zaman makoki hakan yana taka muhimmiyar rawa.
Ya ce: "Wasu Malaman dangane da abun d ake faruwa a yau sun maida hankali wajen musgunawa miliyoyin musulmai a duniya bayan karbar kudi don tallafa wa Yazid da Yazidawa.
Malamin na Pakistan ya yi kira da a kamo kuma a gurfanar da masu tayar da kayar baya a Pakistan saboda cin mutuncin Iyalan Manzon Allah (SAW) da cin zarafin ‘yan Shi’ar kasar, inda ya kara da cewa:“ Irin wadannan kungiyoyin da ayyukansu na cin mutunci sun yi nuni da yanayin tabarbarewar tsaro da zaman lafiyar kasar ne. ”Wadannan ayyuka na iya haddasa rarrabuwar kawuna na addini a kasar da shigar da kasar cikin rikici da hargitsi.
A daya bangaren kuma, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, kowane dan kasar Pakistan yana da 'yancin yin ayyukan ibadarsa," in ji shi, inda ya ambaci wanda ya kafa Pakistan Mohammad Ali Jinnah yana cewa "kowane dan Pakistan yana da' yanci a cikin addininsa." Don haka shigar da kara don gudanar da zaman makoki da jerin gwanon Sayyida Aba Abdullahil Hussain (AS), ya sabawa dokar kasar kuma keta hakkin dan adam ne.
Daga karshe, Dumaki ya yi nuni da cewa: Karamar hukumar lardin Sind ta shigar da kara a kan masu zaman makokin Imam da aka zalunta da yawa kuma a babban mataki na gudanar da zaman makokin jikan Annabin Musulunci (A.S). ) Imam Aba Abdullahil Husain (AS) Ina kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta rufe shari'ar tare da mutunta 'yancin walwala na Mazhabar ' yan Shi'a.



342/