Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) - ABNA ya rawaito, Majalisar Ahlulbaiti (AS) ta kasar Iraki ta fitar da sanarwa ga masu tabligi da wa’azi na kasar du ba da kusantowar lokacin arba'in.
A cikin bayanin ta, Majalisar ta ɗauki tafiya Arbaeen a matsayin tafarkin ɗan adam kuma na duniya wanda ke da jigogi kamar zaman lafiya, alheri, rahama, jinƙai da kyauta, saboda halartar miliyoyin mabiya Ahlul Baiti (AS) a wannan tafarki. yakamata a yi anfani da wannan domin ya zamo an sanar da al'ummar musulmi ga al'adu da dabiu da Ashura ke koyarwa.
A cikin sanarwar, Majalisar ta jaddada bukatar yin sallah a farkon lokaci, mahimmancin kiyaye hijabi da tsabtar jiki, yada alamai na wilaya da bara’a, lura da da’a da barin jayayya, mai da hankali wajen kula da kyakkyawan jiran Imamul Mahdy As, bayyana hadari mamayar al'adun Yammacin Turai ta hanyar intanet da tauraron dan adam, bayyan manyan shubuhohi na wannan zamanin da bada amsar su, aikata ayyukan Husaini ta hanyar kiyaye ka'idodin addini da mahimmancin bayyana matsayin ikon addini a na fadada imamanci, jaddadawa akan soyayya da abota tsakanin mabiya makarantar Ahlul Baiti (AS), musamman tsakanin Iran da Iraki Ya yi gargadin shirin makiya na raba kawunan al'ummomin biyu ta kafofin sada zumunta.
Jaddadawa kan samar da yanayin sallar jam’i a farkon lokaci, kiyaye hijabi da hana haɗewa da juna, gargaɗi game da gasa maras Anfani, da kuma jaddada ruhin haƙuri, hana almubazzaranci da ɓatanci, mahimmancin tsafta a matsayin ɓangaren imani, samun ji na aminci da tsaro da haɗin kai tare da ma’aikatar Tsaro da yaba jarumtawar mayaƙan AlHashdush – Sha’abi na daga cikin buƙatun Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta Iraki daga masu masu jerin gwanon tattakin.
A karshen bayanin ta, Majalisar Ahlulbaiti (AS) ta Iraki ta yi kira ga gwamnatin Iraki da ta sanya aikin tattakin Arbaeen cikin ajandar ta tare da samar da aiyukan taimako da suka dace ga maziyarta a tafarkin Arbaeen, da suka hada da ruwa, wutar lantarki, asibitoci da Kuma yi aikin watsa labarai da ake buƙata na wannan tafiya.
342/