7 Satumba 2021 - 11:16
​Iraki: An Yanke Hukuncin Kisa Kan ‘Yan Ta’adda Na Kungiyar Daesh Dubu 25 Ya Zuwa Yanzu

Kakakin ma’aikatar shari’ar kasar Iraki ya bayyana cewa ana tsare da fursinoni ‘yan ta’adda na kungiyar Daesh kimani dubu 50 a kasar, kuma tuni kotunan kasar sun yake hukuncin kisa kan rabinsu, wato kimani dubu 25 daga cikinsu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : WAA na kasar Iraki ya nakalto Ahmad La’ibi kakkin ma’aikatar shariar kasar ta Iraki ya na cewa dalilin jinkiri wajen aiwatar da hukuncin kisa kan wadanda aka yankewa hukluncin shi ne rashin sanya hannu shugaban kasa Barham Saleh kan takardun hukunce-hukuncen.

Ahmad ya kara da cewa ya zuwa yanzin an aiwatar da hukuncin kasa kan wasu fursinonin da aka yankewa hukuncin kisa ‘yan kadan, amma babu yan kasashen waje da aka zartar da hukuncin kisa a kansa. Akwai ‘yan kasar Faransa 11 daga cikin yayan kungiyar ta Daesh wadanda ake yankewa hukuncin kisa, amma ba’a zartar da hukuncin har yanzu ba.

Ahmad La’ibi ya kammala da cewa babu shakka kan cancantar hukuncin kisa kan kashi 90% daga cikinsu.

Tun bayan shelanta kawo karsheb kungiyar Daesh a kasar ta Iraki a shekara ta 2017 ne aka fara yankewa wadanda suka shiga hannu cikin ‘ayayn kungiyar hukluncin kisa.

342/