Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Rahotanni daga kasar sun ce dakarun rundina ta musaman ce suka hambarar da mulkin shugaba Conde.
A wata sanarwa da sojojin karkashin jagorancin Laftana kanal Mamadou Dounbouya suka karanto a gidan talabijin din kasar, sun ce sun rusa kundin tsarin mulki da kuma rushe gwamnati.
To saidai wasu rahotanni na daban sun ce ma’aikatar tsaron kasar ta sanar da cewa ta murkushe wani yunkurin juyin mulki, tare da kawo karshen barazanar.
Kafin hakan dai wani faifan bidiyo dake yawo a shafukan sada zumunta ya nuno wasu sojoji tare da shugaba Alpha Conde.
Ba’a dai san takamaimai inda shugaban ya ke ba.
Lamarin dai ya biyo bayan da aka jiyo karar harbe harbe a wajajen fadar shugaban kasar a safiyar yau Lahadi.
Mista Conde, dan shekara 83 na shugabancin kasar ta Guinea ne a wa’adi na uku bayan yin tazarce a zaben da aka gudanar bara mai cike da cece-kuce.
342/