5 Satumba 2021 - 10:19
​Najeriya Ba Za Ta Iya Samar Da Likita Guda Ga Ko Wane Dan Kasa 600 Kamar Yadda MDD Take Bukata Ba

Ministan kwadago a tarayyar Najeriya Sen. Chris Ngige ya bayyana cewa Najeriya a matsayinta na kasa mai tasowa ba za ta iya cimma gurin MDD da kuma hukumar lafiya ta duniya WHO na samar da lokita guda ga duk mutane 600 a kasar ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Ministan ya bayyana haka a ranar Jumma’a a lokacinda yake halattar taron watanni uku-uku na majalisar kiwon lafiya ta kasa a Abuja.

Manufar taron na kwanaki biyu dai ita ce tattauna yadda za’a karfafa bangaren lafiya a yankunan karkara na kasar.

Danga karshe ministan ya bayyana cewa Naigeriya ba ta da likitoci a mafi yawan yankunan karkarar kasar, don mafi yawan mutane suna zama a birnin ne. Don haka a halin yanzu a duk fadin kasar ana da likitoci kimani 4000 ne.

Ya ce jami’o’in gwamnati ne kawai suke da asbitocin koyarwa, don haka jami’o’i masu zaman kansa ba sa samar da likitoci a halin yanzun.

342/