5 Satumba 2021 - 10:17
​Ra’isi: Tsaro Da Zaman Lafiya A Kasashe Makobtan Kasar Iran Yana Dai-Dai Da Tsaron Da Zaman Lafiyar Kasar Ne

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana muhimmancin tabbatar da tsaro da kuma zaman lafiya a kasashe makobtan kasarsa, ya kuma kara da cewa zaman lafiya da tsaro mai dorewa a makobta ya na dai-dai da zaman lafiya da tsaro a kasar Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Majiyar muryar jumhuriyar Mususlunci ta Iran ta nakalto Ra’isi ya na fadar haka a tattaunawa kai tsaye da mutanen kasar Iran a jiya da yamma. Ya kuma kara da cewa tun bayan karbar shugabancin kasar ya tattauna da shuwagabnin kasashe kimani 50. A cikin tattaunawar da su ya bayyana anniyar Iran ta hulda da dukkan shuwagabannin da yayi magana da su.

Dangane kasar Afganistan kuma shugaban ya bayyana cewa mutanen kasar Afganistan sun dade suna shan wahala a hannun manya-manyan kasashen duniya, sannan mamayar da Amurka ta yiwa kasar bai amfanesu da kome ba.

Shugaban ya ce idan aka samar da gwamnatin wacce mutanen kasar suka amince da ita, gwamnatinsa a shirye take ta yi hulda da gwamnatin Taliban. Amincewar mutane yana da muhimmanci.

Iran, a ko yauce tana goyon bayan sulhu da zaman lafiya ga mutanen kasar ta Afganistan.

342/