Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, majiyoyin gwamnatin Masar sun sanar da cewa, a yau ne a za a gudanar da zama tsakanin shugabannin Masar Abdulfattah Al sisi, da na Falestine Mahmud Abbas Abu Mazin, da sarkin Jordan Abdullahi na 2, wanda za su gudanar a Sharm Al-sheikh, inda za su tattauna batutuwa da suka shafi wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falastinawa.
A jiya kafofin yada labaran Isra’ila sun sanar da cewa, nan ba da jimawa ba firayi ministan Isra’ila Naftali Bennett zai gana da shugaban kasar Masar AbdulFattah Alsisi a yankin Sharm Al-sheikh na kasar Masar, yayin da wasu ke danganta hakan da zaman na yau.
Sai dai a nata bangaren gwamnatin kasar Masar ta sanar da cewa, a halin yanzu ana tattauna batu yadda za a samu wanzar da zaman lafiya ne tsakanin Isra’ila da Falastinawa, saboda haka maganar ganawa tsakanin Al sisi da Naftali ba ta taso ba a halin yanzu.
Kasar masar dai na daga cikin kasashen ad suka kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila a lokacin mulkin Anwar Sadat, bayan kisan da aka yi wa tsohon shugaban kasar Jamal Abdulnasir.
342/