Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : A rahoton data sba fitarwa watanni uku zuwa uku, game da batun take hakkin dan adam, tawagar ta Minusma, ta ce a tsakanin ranar 1 ga watan Afrilu zuwa 30 ga watan Yuni na bana, an samu karuwar cin zarafin dan adam a Mali da kashi 25 cikin dari.
Kimanin fararen hula 527 aka kashe, ko jikkatawa ko aka sace ko kuma suka bata a tsawon wannan lokaci inji rahoton.
Reshen tawagar ta Minusma kan batun kare hakkin bil adama ya ce yawan mutanen da aka kashe ya karu da kashi 49 cikin dari.
Lamarin ya shafi yankunan tsakiyar kasar ta Mali, da suka hada da : Douentza, Djenne, Bandiagara, Niono, Mopti, Ségou et Koro, sai Gao da Ansongon dake arewacin kasar.
Sai kuma karuwar aikata munanen laifuka a yankunan kudanci da kuma iyakar kasar ta Burkina Faso.
Gungun kungyoyin ‘yan ta’adda da suka hada da GSIM dake da alaka da kungiyar AQMI, da reshen kungiyar IS, su ne ke da alhakin aikata wadanan ayyukan ta’adi, sai kuma sojojin gwamnati wanda rahoton ya ambato cewa suma suna gallazawa fararen hula.
342/