A cewar kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) -ABNA , majiyoyin ma'aikatar lafiya ta Afghanistan sun sanar da cewa adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a kofar tashar jirgin saman Kabul ya kai mutane 170.
Rahotannin wadanda su ka ji rauni kuwa lamarin ya banbanta, inda wasu majiyoyi suka ce adadin wadanda suka jikkata ya kai 150.
Wani janar na Amurka daga ma'aikatar tsaro ta Pentagon ya tabbatar da cewa sojojin Amurka 13 ne suka mutu yayin da wasu 15 suka samu raunuka a hare -haren kunar bakin wake biyu da aka kai a filin jirgin saman Kabul da ake zargi da ISIL ne.
Wannan shi ne asarar rayuka ta farko da Amurka ta yi a Afghanistan tun watan Fabrairu 2020 kuma mafi zubar da jini cikin shekaru goma.
Ba a ba ‘yan jarida damar ba da labarin abin da ya faru ba saboda iykoki da kungiyar Taliban ta sanya.
Kungiyar ta'adda ta ISIS ta dauki alhakin kai harin kunar bakin waken na filin jirgin saman Kabul, inda ta yi ikirarin cewa sojojin Amurka da kawayenta ne suka kai harin.
Kafafan yada labarai na Afganistan sun nakalto sojojin Amurka suna fadar haka a jiya Asabar cewa jiragen yakin Amurka mara sa matuki sun kai hari kan wani da ake zargin shirya kai harin na kungiyar ISIL a lardin Nangarhar kuma an kashe shi a harin.
342/