20 Agusta 2021 - 14:07
Mutane uku sun yi shahada tare da jikkata 12 a harin da sojojin Najeriya suka kai kan masu juyayin Ashura

Hare -haren sojojin Najeriya kan masu makoki a jihar Sokoto ya yi sanadiyar samun shahidai Uku tare da jikkata mutum 12.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti (AS) - ABNA - ya rawaito, jami'an tsaron Najeriya dauke da makamai sun kai hari kan masu zaman makoki a ranar Ashura a jihar "Sokoto" inda suka far musu da harsasan yaki. A wannan farmakin na matsorata da aka kai ranar Alhamis 19 ga watan Agusta, 1400 (ranar goma ga watan Muharram 1443), mutane uku sun yi shahada tare da jikkata mutum 12, daga cikinsu an ba da rahoton cewa suna cikin mawuyacin hali.

Harin da jami'an tsaro suka kai ya tarwatsa bikin kuma masu juyayin Husain suka watse.

Ya kamata a sani cewa zaman makokin Ashura a Sakkwato, Najeriya, an fara shi cikin lumana tun farko kuma babu wata matsala data faru Kamar yadda aka gudanar da zamomin cikin lumana a garuruwa da dama na wannan kasa kuma an kammala ba tare da wata matsala ba.

342/