18 Agusta 2021 - 13:45
Nijar : An Fara Zaman Makoki Na Kwanaki Biyu Bayan Kisan Mutane 37

Gwmanatin Jamhuriyar Nijar ta ayyana zaman makoki na kwanaki biyu daga yau Laraba, domin juyayin mutum 37 da suka rasa rayukansu a wani harin da ‘yan bindiga suka kai a jihar Tillabery.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA : A wata sanarwa da t afitar da yammacin jiya, ta hanyar kafofin talabijin da radiyo na kasar, gwamnatin ta ce za’a rage tsawon tutoci domin juyayin wadanda suka rasu a harin.

Harin dai da wasu ‘yan bindiga kan Babura dauke da manyan makamai suka kai da yammacin ranar Litinin lokacin da suke aiki a gonakinsu ya yi sanadin mutuwar fararen hula 37 a kauyen Darey Dey, dake lardin Banibangou a yankin Tillabery.

A shekarun baya bayan nan yankin Tillabery yana fuskantar karuwar munanan hare-hare da ake kaddamarwa kan dakarun tsaron kasar da kuma fararen hula.

Daga farkon shekarar 2021, kimanin fararen hula 300 aka kashe a yankin, kamar yadda alkaluman hukumomi suka bayyana.

342/