ABNA24 : Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta Nakalto wakilin France 24 yana fadar haka, ya kuma kara da cewa jiragen yaki suka harbi kan mayakan na Taliban a cikin birnin, amma suna ci gaba da fafatawa da sojojin gwamnatin kasar a kan tituna da lungunar birnin.
A jiya Jumma’a ne sojojin na Taliban suka shiga Qandus, kafin haka sun kwace iko da babban biranin wasu larduna gudabiyu.
Tun cikin watan mayun da ya gabata ne, wato a lokacin da sojojin kasashen waje suka fara janyewa daga kasar Afganistan Taliban ta fara kwace kasar daga hannun gwamnatin kasar a hankali a hankali.
342/