1 Agusta 2021 - 16:38
UAE Ta Mayar Wa Shugaban Majalisar Dokokin Tunisia Da Martani Mai Zafi

Gwamnatin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE ta mayar wa shugaban majalisar dokokin kasar Tunisia da martani mai zafi, dangane da zargin cewa tana da hannu a abin da ke faruwa a kasar.

ABNA24 : Tashar Alalam ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ya wallafa a shafinsa na twitter, babban mataimakin shugaban kasar UAE kan harkokin siyasar kasa da kasa Anwar Qarqash ya bayyana cewa, furucin shugaban majalisar dokokin Tunisia dangane da UAE ba abu ne da za su lamunta da shi ba.

Ya ce kasarsa ba da hannu a abin da yake faruwa a Tunisia, kuma maimakon zargin kasarsa, zai fi kyau ga bangarorin siyasar kasar da suka nuna gazawa har al’ummar kasar suka gane, da su dawo su yi karatun ta natsu domin gyara kuakuransu.

A wata zantawa da shugaban majalisar dokokin kasar ta Tunisia Rashid Ganushi ya yi da jaridar Times ya bayyana cewa, gwamnatin UAE ce take da hannu dumu-dumu a cikin dukkanin matsalolin siyasa da ake fama da su yanzu a kasar Tunisia.

Ganushi ya kara da cewa, wannan yana daga cikin shirin UAE na rusa dukkanin nasarorin da ya ce an samu a lokacin boren da ya wakana a kasashen larabawa.

A ranar Lahadin makon da ya gabata ne dai shugaban kasar Tunisia Qais Saeed ya sanar da dakatar da majalisar ministoci gami da Firayi ministan, kamar yadda kuma ya sanar da dakatar da ayyukan majalisar dokokin kasar har sai abin da hali ya yi.

342/