31 Yuli 2021 - 14:57
WHO: Zai Yi Wahala A Samu Kaso 10 Na Al’ummar Afirka Da Za Su Samu Riga Kafin Korona Kafin Karshen Bana

Hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadin cewa, kaso 1.5 na al’ummar Afirka ne kadai suka samu riga kafin cutar COVID-19, Kana akwai yiwuwar nahiyar ba za ta kai matakin kaso 10 ba zuwa watan Disamban bana, duk da cewa WHO na son tsallake wannan mataki a watan Satumba.

ABNA24 : Babban mashawarcin Darakta Janar na hukumar WHO, Bruce Aylward, ne ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai, inda ya ce, yanzu haka, ba a kama hanyar kai wa ga samun kaso 10 na al’ummar Afirka da suka karbi riga kafin ba kafin karshen bana.

Ya ce ya kamata wannan ya zama abun damuwa, yana mai cewa adadin wadanda cutar ke kashewa a nahiyar ya karu da kaso 80.

A cewar WHO, kasa da kaso 2 kacal nahiyar ta samu, cikin alluran riga kafin COVID-19 biliyan 4.07 da aka yi amfani da su a duniya baki daya.

342/