ABNA24 : A cikin bayanin na rundunar sojin kasar ta Rasha, ya zuwa yanzu haka an kwaso ‘yan ta’adda Daesh masu yawa daga Syria da Libya zuwa Afghanistan, kuma ana ci gaba da aikin jigilarsu.
Bayanin ya kara da cewa, tun daga lokacin da Amurka ta sanar da shirinta na janye sojojinta daga kasar Afghanistan ne jigilar ‘yan ta’addan Daesh ta karu cikin sauri daga Syria da Libya da ma wasu kasashen duniya zuwa Afghanistan.
A nata bangaren mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, suna wadatattun dalilai kan cewa, mayakan ‘yan ta’adda na Daesh suna da kyakkayawar alaka da Amurka, kuma suna gudanar da ayyuka a tare.
Ko a kwanakin baya shi ma ministan harkokin wajen kasar rasha Sergey ya sanar da cewa, sun samu cikakkun bayanai kan yadda Amurkawa suke yin aiki tare da ‘yan ta’adda na kungiyar Daesh.
342/