ABNA24 : Mista Mahamat, ya ce rikicin wanda aka shafe sama da shekaru 70, za’a iya warware shi ne kawai ta hanyar kafa kasashe biyu masu cin gashin kansu.
A cewar Mahamat, ba iya hanyar da za ta tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali daga dadadden rikicin kadai ya kamata a bi ba, har ma ya dace a tabbatar da kare hakkokin kowane bangare.
Ya ce kungiyar ta Afrika, a cikin shekaru kusan sittin a tarihin kafuwarta, ta sha nanata aniyarta game da batutuwan dake shafar rikicin Falastinawa da Isra’ila cewa, kafa kasashe biyu masu cin gashin kai ita ce sahihiyar hanyar da za ta tabbatar warware rikicin da kuma samun dorewar zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu.
A kwanan nan ne dai kungiyar tarayyar Afrika, ta amince da dawowar Isra’ila a matsayin mamba ‘yar sa ido a kungiyar ta AU, saidia lamarin bai yi Falasdinu dadi ba.
342/