25 Yuli 2021 - 17:19
Majalisar Saliyo Ta Kaɗa Kuri’ar Soke Zartar Da Hukuncin Kisa A Кasar

Majalisar ƙasar Saliyo ta kaɗa kuri’ar amincewa da ƙudurin da aka gabatar mata na soke zartar da hukuncin kisa a ƙasar sama da shekaru ashirin bayan da ƙasar ta zartar da hukuncin kisa na ƙarshe a ƙasar.

ABNA24 : Rahotanni daga ƙasar sun ce a zaman da ‘yan majalisar suka gudanar a jiya Juma’a, mafi yawa daga cikin ‘yan majalisar sun kaɗa kuri’ar amincewa da batun soke zartar da hukuncin kisa a ƙasar.

A halin yanzu dai ana jiran shugaban ƙasar Julius Maada Bio ne ya sanya hannu kan ƙudurin dokar don ta zama doka, wanda hakan zai sanya ƙasar Saliyon ta zama ƙasar Afirka ta 23 da za a soke dokar zartar da hukuncin kisa a ƙasashensu.

Idan dai har ƙudurin ya zama doka, hakan yana nufin za a mayar da hukuncin laifuffuka irin su kisa ko tawaye da a suke da hukuncin kisa zuwa ga ɗaurin rai da rai ko kuma ɗaurin shekaru 30 zuwa sama.

Tun daga shekara ta 1998 zuwa yau ba a zartar da hukuncin kisa ba a ƙasar ta Saliyo, wato tun bayan hukuncin kisan da aka zartar kan wasu sojoji su 23, sai dai kuma duk da hakan ƙasar Saliyon wacce har ya zuwa yanzu take ƙoƙarin farfaɗowa daga yaƙin basasan da ya faru a ƙasar tana ci gaba da fuskantar suka daga ƙungiyoyin masu ikirarin kare haƙƙoƙin bil’adama sakamakon ci gaba da barin hukuncin kisan a cikin kudin tsarin mulkin ƙasar.

Ya zuwa yanzu dai akwai mutane 99 da suke tsare a gidajen yari waɗanda kuma aka yanke musu hukuncin kisa a ƙasar ta Saliyo saboda samunsu da laifuffuka da suka jiɓinci fashi da makami da kuma kisan kai.

342/