24 Yuli 2021 - 06:21
​Siriya: ‘Yan Ta’adda Sun Fasa Bututun Iskar Gas A Gabashin Kasar A Safiyar Yau Jumma’a

Wasu ‘yan bindiga wadanda har yanzun ba’a san ko suwa ye ba sun fasa bututun iskar gas a lardin Deir-Zur na gabacin kasar Siriya a safiyar yau Jumma’a.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya bayyana cewa button da aka fasa kuma ya kama da wata, ya na daukar iskar gas daga garin Hasaka zuwa birnin Homs dake tsakiyar kasar ta Siriya ne.

Labarin ya kara da cewa wannan ba shi ne karon farko wanda ‘yan ta’adda suke kokarin fasa bututun ba.

Tun shekara ta 2011 ne gwamnatin kasar Amurka da kawayenta na yankin wadanda suka hada da gwamnatin kasar Saudiyya da Turkiyya su ke kokarin kifar da gwamnatin shugaban Bashar Al-Asad na kasar Siriya don bawa Isara’ila karfi a yankin, amma basu sami nasara ba.

342/