ABNA24 : A wata sanarwa da hukumar gidan yarin ta fitar ta ce an amince da buƙatar hutun da tsohon shugaba Zuma ya buƙata don halartar jana’izar ƙanin nasa, yana mai cewa a yayin hutun ba sai tsohon shugaban ya sanya tufafin gidan yari ba.
A Afirka ta Kudun dai a mafi yawan lokuta a kan bar fursunoni su halarci jana’izar danginsu da suka rasu matuƙar dai babu wani hatsari a cikin hakan.
Кanin Jacob Zuman mai suna Micheal ya mutu ne yana ɗan shekaru 77 a duniya bayan doguwar rashin lafiyar da yayi fama da ita kamar yadda kafafen watsa labaran ƙasar suka bayyana.
A watan da ya gabata ne wata kotu a ƙasar Afirka ta Kudun ta ɗaure Jacob Zuma, ɗan shekaru 79 a duniya zaman gidan yari na tsawon watanni 15 bayan ta same shi da laifin raina kotu sakamakon ƙin bin umurnin da aka yi masa na ya gurfana a gaban wani kwamitin binciken zargin rashawa da cin hanci da ake wa gwamnatinsa a lokacin da yake mulki.
Ɗaurin da aka yi wa tsohon shugaba Zuman dai ya haifar da rikici da zanga-zangogi a lardinsu na Kwa-Zulu Natal lamarin da daga baya ya rikiɗe ya zama tarzoma da satar kayayyakin jama’a.
342/