ABNA24 : Wannan buƙatar na cikin ƙudurin da majalisar ta ɗauka ne a zaman da ta gudanar don tattauna batutuwa daban-daban ciki kuwa har da matsalar tsaro da yake ci gaba da ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya.
Wannan ƙudurin kuwa ya biyo bayan wasu shawarwari guda 19 ne da kwamitin na musamman kan harkokin tsaro na majalisar da ke ƙarƙashin shugaban majalisar Femi Gbajabiamila ya gabatar bayan tarurrukan da ya gudanar a baya.
Wani ɓangare na rahoton kwamitin ya ƙumshi gaggauta ba wa ‘yan sanda horo na musamman don faɗa da matsalar rashin tsaro da ake fuskanta, inda majalisar ta buƙaci gwamnatin da ware wasu ‘yan sanda na musamman su 40,000 da za a ba su horo na musamman inda daga nan za a tura wa kowace jiha ta ƙasar guda 1000 daga cikinsu don su gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro a can, sannan sauran da suka saura kuma a sake rarraba su tsakanin yankunan arewa masu gabas, kudu maso yamma da kuma kudu maso gabas na ƙasar saboda a nan ne aka fi fuskantar matsalar tsaron.
Har ila yau kuma majalisar ta buƙaci a samar da wata tawagar ‘yan sanda waɗanda za su ba wa masu kula da dazuka a Najeriyan horo na musamman da kuma aiki tare da su don tabbatar da tsaro a dazukan da ake da su a Najeriya waɗanda a nan ne aka fi aikata ayyukan laifi da yin garkuwa da mutane.
342/