ABNA24 : a yau Jami’an Gwamnatin kasar Afghanistan sun sanar da cewa, jami’an tsaron kasar sun halaka Kari Shaghasi, shugaban bangaren leken asiri na kungiyar Taliban.
Bayanin ya ce, jami’an tsaron sun dana masa wani tarko wanda ya fada a ciki, inda suka halaka shi cikin sauki a cikin Lardin Loghar, tare da kame wasu daga cikin wadanda suke tare da shi.
A cikin ‘yan kwanakin na dai musamman a makon da ya gabata, kungiyar Taliban ta mamaye yankuna da dama a cikin kasar Afghanistan, inda ta shimfida ikonta, tare da kakkabe hannun gwamnatin kasar daga wadannan yankuna.
Wannan dai yana zuwa a daidai lokacin da Amurka ta sanar da fara janye sojojin da ta jibge a kasar, tun bayan yakin da ta kaddamar a kasar shekaru 20 da suka gabata, da sunan murkushe kungiyar ta Taliban.
A cikin makon da ya gabata dai an gudanar da wata tattaunawa a birnin Tehran na kasar Iran, tsakanin wakilan gwamnatin Afghanistan da kuma na kungiyar Taliban, gami da sauran bangarori na siyasa da kuma na al’umma a kasar ta Afghanistan.
Manufar tattaunawar da ita ce lalubo hanyoyi na samun fahimtar juna tsakanin dukkanin bangarorin kasar, domin kaucewa fadawar kasar cikin wani yanayi mafi muni bayan janyewar sojojin mamaya daga kasar.
342/