10 Yuli 2021 - 13:09
Rwanda Za Ta Tura Da Dakaru Zuwa Кasar Mozambique Don Taimakawa Кasar Faɗa Da Masu Ikirarin Jihadi

Gwamnatin ƙasar Rwanda ta sanar da cewa za ta tura dakarun ƙasar da suka haɗa da sojoji da ‘yan sanda zuwa lardin Cabo Delgado na ƙasar Mozambique da ke fama da rikice-rikicen masu ikirarin jihadi a ƙasar.

ABNA24 : A jiya Juma’a ce dai gwamnatin Rwandan ta sanar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce dakarun nata wanda adadinsu zai kai mutum 1000 za su yi aiki kafaɗa da kafaɗa ne da dakarun ƙasar ta Mozambique da kuma sauran dakarun da ƙungiyar ci gaban ƙasashen Kudancin Afirka (SADC) suka tura ƙasar.

Tun a shekara ta 2017 ne dai yankin arewacin ƙasar Mozambique din yake fuskantar gagarumar matsalar tsaro sakamakon ayyukan ‘yan ƙungiyoyin da suke da alaƙa da ƙungiyar ta’addancin nan ta ISIS waɗanda suke kai hare-hare arewacin garin Palma lamarin da ya tilasta wa mutane wajen gudu su bar shi.

A watan da ya gabata ne dai shugabannin ƙasashen ƙungiyar SADC suka yarda su tura sojoji ƙasar Mozambique ɗin don taimaka mata faɗa da ‘yan ta’addan.

342/