ABNA24 : Wakilai daga ‘yan siyasar kasar ta Libiya, basu samu cimma matsaya ba game da zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisar dokokin Libiya da ake fatan gudanarwa a watan Disamba mai zuwa a cewar sanarwar da tawagar ta fitar a cikin daren jiya.
A halin da ake ciki dai akwai rashin tabbas game da makomar tattaunawar ta tsakanin ‘yan Libiyar, kuma hakikanin gaskia ‘yan Libiya ba zasu ji dadin wannan labarin ba, inji mukadashin sakatare janar na tawagar MDD kan rikicin Libiya, Raisedon Zenenga.
Dama dai Babban abunda tattaunawar ta sanya a gaba, shi ne samun fahimtar juna tsakanin ‘yan siyasar na Libiyar kafin ranar 1 ga watan Yulin nan, domin shirya babban zaben kasar mai cike da mahimmanci ga kasar ta Libiya.
342/