1 Yuli 2021 - 11:56
​Kwamitin Bincike Kan Rawar Da Sojojin Faransa Suka Take A Kisan Kiyashin Tutsi Ya Mika Rahoton Bincike Ga Paul Kagami

Kwamitin bincike wanda shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kafa a shekara 2019 don binciken rawar da sojojin kasar Faransa suka taka a kisan kiyashin da aka yiwa ‘yan kabilar Tutsi a kasar Rwanda a shekara 1994 ya kai ziyarar aiki na mako guda a kasar ta Rwanda.

ABNA24 : Jaridar New Times ta kasar Rwandan ta bayyana cewa Vincent Duclert wani masanin tarihi dan kasar Faransa da tawagarsa sun kammala aikin binciken da aka basu, har kuma sun mikawa shugaban Macron sakamakon binciken nasu a ranar 26 ga watan Maris na wannan shekara.

Labarin ya kara da cewa shugaban kasar Rwanda Paul Kagami ya sami kofin rahoton binciken shima a cikin watan Afrilun da ya gabata. Vincent da tawagarsa sun zo kasar Ruwanda ne fiye da mako guda da ya gabata inda suka ziyarci wasu wuraren da aka yi kissan kiyashin, da kuma ganawa da wadanda kisan kiyashin ya shafa da kuma iyalan wadanda aka kashe.

An kashe mutane kimani miliyon guda, mafi yawansu yan kabilar Tutsi tsiraru a kasar ta Rwanda a lokacin. Sojojin kasar Faransa suna cikin kasar kuma suna iya yin wani abu don haka hakan faruwa amma basu yi ba.

342/