28 Yuni 2021 - 13:41
Aƙalla Mutane 30, Ciki Har Da Fararen Hula 13 A Wani Harin Da Al-Shabab Ta Kai Somaliya

Rahotanni daga ƙasar Somaliya sun bayyana cewar alal aƙalla mutane 30 sun rasa rayukansu ciki kuwa har da fararen hula 13 a lokacin da ‘yan ƙungiyar ta’addancin nan ta Al-Shabab suka kai garin Galmudug na ƙasar Somaliyan.

ABNA24 : Kafafen watsa labarai sun jiyo wani jami’in tsaro na yankin Manjo Mohamed Awale yana tabbatar da labarin harin in da ya ce ‘yan ta’addan sun kai harin ne kan wani sansanin soji da ke garin na Galmudu lamarin da yayi sanadiyyar musayen wuta tsakaninsu da sojojin da kuma mutanen gari.

Jami’in ya ƙara da cewa an kai harin ne ta hanyar amfani da wasu motoci guda biyu da aka maƙare su da bama-bamai da kuma amfani da bindigoyi a gumurzun da ya ɗau sama da sa’a guda ana yi.

Manjo Awale ya ci gaba da cewa yayin harin dai mutane 30 da suka haɗa da sojoji 17 da kuma fararen hula 13 ne suka rasa rayukansu baya ga waɗanda suka sami raunuka, sai dai yace an samu nasarar fatattakan ‘yan ta’addan biyo bayan ɗaukin da mutanen gari ɗauke da makamai suka kawo barikin sojin.

Кungiyar Al-Shabab ɗin ta ɗauki alhakin kai hari tana mai cewa dakarunta sun kashe sama da sojoji 30 da kuma raunana wasu sama da 40.

342/