ABNA24 : Kwamitin ya kuma nuna kin amincewarsa akan sojojin dake rike da mulki su shiga zaben da aka shirya gudanarwa a watan Fabrairun 2022 mai zuwa, kamar yadda sojojin sukayi alkawari.
Jakadan Faransa a MDD Nicolas de Riviere, ya ce ''babban abin da ya kamata a bai wa fifiko shi ne shirya zaben shugaban kasa a Mali a badi’’
Shi ma wakilin MDD na musamman a Mali El-Ghassami Wane, ya yi kira ga kasashen duniya da su zo a hada karfi don ceto Mali daga halin rashin tsaro da kuma matsalolin da suka dabaibaye kasar.
Kasar Mali, dai ta fusknaci juyin mulki har sau biyu a cikin watanni tara, karkashin jagorancin Kanar Assimi Goita, wanda kwanan nan ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya, ya kuma nada jagoran adawa Choguel Maiga a matsayin Firaminista.
342/