16 Yuni 2021 - 13:25
China Ta Bukaci Kungiyar Nato Ta Shiga Taitayinta

Kasar China, ta mayar wa da kungiyar tsaro ta Nato da martanin cewa ta shiga tafiye tafiyanta, bayan da kungiyar ta zargi kasar da cewa tana take taken fadada shirinta na nukiliya.

ABNA24 : Nato dai ta zargi gwamnatin Beijing da cewa take-takenta na fadada makamashin nukiliya ya saba wa dokar tsaro ta kasa da kasa.

China ta ce tsarin tsaronta na kare kai ne, kuma bai kamata kungiyar ta Nato, ta maida hankali kan batutuwan siyasa da ba su da tushe.

Saidai a zantawarsa da manema labarai, shaugaban NATO, Jens Stoltenberg ya ce, ba zu da niyar shiga sabon yakin cacar-baka kuma China ba abokiyar gabarsu ba ce a cewarsa.

342/