14 Yuni 2021 - 09:42
Iran Ta Aike Wa Da Afghanistan Taimakon Bututun Iskar Oksijin ( Oxygen ) Domin Taimakawa Da Masu Fama Da Cutar Corona

Ministan kiwon lafiya na kasar Afghanistan Wahid Majruh ne ya sanar da cewa; kasashen Iran da Uzbekistan sun aika wa kasar tasa da taimakon bututu mai yawa na iskar ta oksijin da ake amfani da ita wajen fada da cutar corona.

ABNA24 : Wahid ya ci gaba da cewa; A kowace rana ta AllahIran din tana aike wad a bututun na iskar oksijin zuwa gabashi da kuma yammacin kasar ta Afghanitsan.

Har ila yau ministan kiwon lafiyar na kasar Afghanistan ya ce; kasar tasa ta kuma kulla yarjejeniya da kasar Uzbekistan domin aike ma ta da wasu bututun na iskar oksijin guda 300 domin yi wa wadanda su ka kamu da cutar corona magani.

342/