ABNA24 : Kiran wanda ya fito daga kungiyoyi masu kishin Palasdinu ya bukaci ganin an daga tutocin Palasdinu kadai ba na kungyoyi ba a duk inda za a yi gangamin ko taro na nuna fushi a cikin gida da kuma sansanonin ‘ yan gudun hijira.
Har ila yau, wadanda su ka yi gayyar domin gudanar da tarukan sun kira yi dukkanin masu son adalci a duniya da su kasance a tare da al’ummar ta Palasdinu wajen fafutukar da take yi na neman a yi ma ta adalci wajen takawa ‘ yan sahayoniya birki da su daina tsokanar da suke yi a birnin Kudus, da zai zama musabbabin sake barkewar wani sabon rikici.
342/