12 Yuni 2021 - 10:34
​Iran Da Kasar Girka Zasu Fara Aiki Tare A Fagen Wasanni

A wata ganawa da karamin ministan a ma’aikatar al’adu da wasanni na kasar Girka, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasar Iran Reza Salehi Amiri ya bukaci kasashen biyu su kulla yarjejeniya ta hadin guiwa a wasu wasanni.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press(IP) ya nakalto Amiri ya na fadar haka a jiya jumma’a a lokacinda ya kai ziyarar aiki a birnin Athens babban birnin kasar Girka. Amiri ya kara da cewa kasashen Iran da Girka su na ta tarihi mai tsawo a fagen wasannin, don haka baya ganin akwai wani abinda zai hana kasashen biyu kulla wata fahintar juna a wannan bangaren.

A nashi bangaren karamin ministan al’adu da wasannin na kasar Girka, Lefteris Avgenakis ya ce babu laifi kasashen biyu su kulla wata yarjejeniya ta aiki tare a bangaren wasanni a tsakaninsu.

342/