6 Yuni 2021 - 13:46
Mutane 100 Ne Masu Ikirarin Jihadi Su Ka Kashe A Kasar Burkina Faso

Rahotannin da suke fitowa daga kasar ta Burnika Faso,sun ambaci cewa; A daren jumaá wayewar garin jiya Asabar ne masu ikirarin jihadin su ka kai hari a garin Sohlan dake arewacin kasar ta Burnkia Faso. A tashin farko ‘yan taáddar sun kai hari akan wuraren bincike na masu sanya kai na kungiyar kare kasa, sai kuma su ka kai wa fararen hula masu taimakawa sojoji hari daga nan kuma sai su ka fara kai harin kan mai uwa da wabi.

ABNA24 : Maharan sun kuma cinnawa gidajen mutane da kasuwannin yankin wuta.

Wani jamiín sojan kasar ta Burkina Faso ya shaidawa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa; Wadanda aka kashe din sun hada maza da mata, kuma bayanan farko sun kai 100

Gwamnatin kasar ta tabbatar da afkuwar harin wanda shi ne mafi mufi da masu ikirarin jihadi su ke kai a kasar tun 2015.

Makwanni biyu da su ka gabata ma an kai wasu hare-haren taáddancin a wannan yankin, da su ka yi sanadin mutuwar mutane 4.

Gwamnatin kasar ta sanar da zaman makoki na saói 72 daga ranar Asabar zuwa Litinin.

342/