18 Mayu 2021 - 11:36
​5G Ta Fara Sauya Yadda Masu Amfani Da Wayoyin Tafi Da Gidanda Suke Amfani Da Su

A wani bincike wanda kamfanin sadarwa na Ericsson ConsumerLab ya gudanar ya gano cewa tsarin samar da yanar gizo na G5 ya fara sauya rayuwar mutane wadanda suke amfani da tsarin na G5 a kasashen duniya da dama.

ABNA24 : Jaridar Egypt Daily ta bayyana cewa tuni tsarin yanar gizo mafi karfi a duniya wato G5 ya fara sauya rayuwar masu amfani da shi a kasashen duniya da dama, daga cikin tsarin ya sa suka rage amfani da tsarin samar da yanar gizo wanda ake kira WiFi a gidajensu, don irin karfi da kuma saurin biyan bukatu wanda tsarin na G5 yake bayarwa.

Kamfanin Ericsson ConsumerLab ya ce, ya gudanar da bincike a wasu kasuwannin kamfanin 26 a kasashe daban-daban, wadanda kuma suka hada da Amurka, Cana, Kurea ta Kudu, da kuma Burtania, inda ya gano cewa duk 1 daga cikin mutane 5 masu amfani da G5 sun rage amfani da Wifi a gidajensu.

Labarin ya kara da cewa, ya zuwa yanzu a cikin mutane kimani biliyon 1.3 masu amfani da wayar salula a duniya, miliyon 220 daga cikinsu suna amfani da tsarin yanar gizo na G5 ne. Daga karshe rahoton ya kammala da cewa tsarin bada internet na G5 ya samu Karin karbuwa ne a lokutan kulle wadanda ake ta yi a kasashen duniya saboda hana yaduwar cutar korona.

342/