ABNA24 : Daga cikin shugabannin kasashen da suke halartar taron da akwai na Masar, Rwanda, Senegal, Ethiopia, Ghana, da Nigeria.
Bugu da kari, kungiyar tarayyar Afrika ta aike da tata tawagar zuwa wajen taron.
Shugaban kungiyar tarayyar Afirka Musa Faki ya bayyana cewa:
“ Sakon dake cikin wannan taron shi ne cewa ba za mu bar kasar sudan ita kadai ba tana fuskantar kalubale saboda yanayin sauyi da take ciki. Ina kuma yin jinjina da samari da matan kasar Sudan na son samar da sauyi.”
A jiya Litinin taron na kasar Faransa ya mayar da hankali ne akan kasar Sudan da yadda za a taimaka mata a yanayin da take ciki na rikon kwarya.
A jawabin da Pira ministan kasar Sudan Abdalla Hamduk ya yi, ya yi ishara da bukatar gina tattalin arziki mai karfi, maimakon barin samarin kasar masu hazaka suna mutuwa a tekun Mediterranea, akan hanyar yin hijira zuwa turai.
342/