ABNA24 : Tashar talabijin ta presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Ori Gordin ministan tsaron cikin gida na HKI ya na fadar haka a jiya Lahadi. Ya kuma kara da cewa ya zuwa yanzu, rokoki akalla 3000 ne kungiyoyi masu gwagwarmaya na Hamas da Jihadul Islami suka cilla kan garutuwan yahudawan Isra’ila.
Janar Gordin ya ce a yakin shekara ta 2006 da kungiyar hizbullah rokoki 4,500 aka cilla kan yahudawan.
Tun ranar litinin da ta gabata ce kungiyoyin suka fara maida martani da rokoki wadanda suka jawo asarori na rai da dukiya masu yawa ga HKI ya zuwa yanzu.
Sannan falasdinawa kimani 200 ne suka yi shahada, 55 daga cikinsu yara, 33 mata, sannan wasu 1230 kuma suka ji rauni.
342/