ABNA24 : Sadr ya bukaci a kiyaye ka’idojin kiwon lafiya saboda hana yaduwar cutar korona a gangamin nay au Asabar, sannan ya dole ne a daga tukar kasar Falasdinu, sannan a kona tutocin Isra’ila da Amurka mai goyon bayanta.
A wani labarin kuma Khalid Mash’al shugaban bangaren siyasa na kungiyar Hamas a wajen kasar Falasdinu da aka mamaye, ya bayyana cewa dole ne a kiyaye sharuddun tsagaita bude wuta tsakanin kungiyarsa da sojojin Isra’ila a duk wata tsagaita bude wuta da za’a yi nan gaba.
Khalid Mash’al ya kuma kara da cewa dole ne a dakatar da korar falasdinawa a unguwar sheikh Jarrah wanda ya haddasa rikici na baya-bayan nan. Sannan a cire duk shingaye masu hana Falasdinawa isa masallacin Al-Aqsa da kuma sakin duk Falasdinawan da aka kamma a baya-bayan.
342/