ABNA24 : Ma’aikatar ta bukaci jami’an tsaron kasar Iraki su kare wuraren jami’an diblomasiyyar kasar Iran da suke kasar Iraki daga yan zauna gari banza wadanda ake amfani da su don rikita harkokin zamantakewa a kasashen biyu.
Jakadan kasar Iraki a Tehran, a wannan ganawar ya kara tabbatar da cewa kasar Iraki zata ci gaba da kare wuraren jami’an diblomasiyya a kasar kamar yadda dokokin kasa da kasa suka zayyana, kuma ya bayyana takaicinsa kan abinda ya faru a karbala.
Da farko dai wasu matasa ne suka fara zanga-zangar yin allawadai da Iran a cikin haramin Imam Husain (a) kafin su je karamin ofishin jakadancin kasar Iran suka kona tayoyi kusa da shi, kafin jami’an tsaron kasar Irako su tarawatsa su.
Amma hotunan da suka dauka na kona tayoyin sun yadu a tashoshin talajin na kasashen larabawa da dama, da nufin yada kiyayyar Iran a kasar Iraki.
342/