ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, a wata zantawa da manema labarai a birnin Mugadishu, ministan yada labarai na kasar Somalia Abdulrahman Yusuf ya bayyana cewa, an samu daidaito da fahimtar juna tsakaninsu da kasar Kenya.
Ya ce gwamnatin kasar Qatar ce ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin an kawo karshen tayar da jijiyoyin wuya da ke yi tsakanin Somalia da Kenya a kan batun mallakar wasu wurare da ke kan iyakokin kasashen biyu, da suke da arzikin danyen man fetur da iskar gas.
Ita ma a nata bangaren ma’aikatar harkokin wajen kasar Kenya ta sanar a cikin wani bayani da ta fitar a jiya cewa, alaka za ta ci gaba a tsakaninsu da Somalia, da hakan zai shafi kara karfafa hulda a bangaren harkokin kasuwanci, sadarwa, sufuri, da kuma sauran bangarori da suka shafi bunkasa al’adu na kasashen biyu makwabtan juna.
Kamar yadda kuma gwamnatin ta Kenya ta nuna jin dadinta kan yadda kasar Qatar ta taka rawa wajen ganin an samu sulhu da fahimtar juna a tsakaninta da kasar Somalia.
Ministan harkokin wajen kasar Qatar Muhammad Bin Abdulrahman Al-thani ya bayyana cewa, Qatar tana maraba da hadin kan da dukkanin kasashen biyu na Somalia da Kenya suka bayar, wajen ganin cewa shiga tsakanin da ta yi ya kai ga cimma nasara.
342/