5 Mayu 2021 - 14:35
Bangaren Sojan Kungiyar Hamas, Na “Rundunar Kassam” Ya Ja Kunnen HKI Da Ta Datakar Da Harin Da Take Kai Wa Birnin Kudus

Kwamandan rundunar ta “Kata’ibul-Kassam” Abu Khalid Muhammad al-Dhaifh, ne ya yi wa ‘yan sahayoniyar gargadin a jiya Talata da marece akan harin da suke kai wa Palasdinawa mazauna unguwar al-Jarrah dake cikin birnin Kudus.

ABNA24 : Al-Dhaif ya ci gaba da cewa; Jagororin gwagwarmaya da dakarun kassam, suna kallon abinda yake faruwa daga kusa, sannan ya ci gaba da cewa; Idan har ba a dakatar da harin da ake kai wa ‘yanuwanmu a unguwar Jarrah ba, to ba za mu nade hannuwanmu mu zama ‘yan kallo ba, masu kai harin za su dandana kudarsu.”

Tun a farkon watan Ramadan ne dai yahudawan sahayoniya su ke kai wa unguwar jarrah hari, da takura musu a lokutan salloli sannan kuma da kokarin tilasta musu yin hijira daga unguwar tasu.

342/