4 Mayu 2021 - 14:28
​Iran Ta Ce A Shirye Take Domin Gudanar Da Tattaunawa Tare Da Saudiyya

Gwamnatin kasar Iran ta sanar da cewa a shirye take domin gudanar da tattaunawa tare da gwamnatin Saudiyya a kowane irin mataki.

ABNA24 : Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Saeed Khatib Zadeh ne ya bayyana hakan a yau, inda ya ce Iran tana maraba da sauyin da aka samu na kalaman jami’an gwamnatin Saudiyya dangane da alaka a tsakaninsu.

Ya ce Iran din a shirye take domin gudanar da tattaunawa tare da Saudiyya, domin warware batutuwa da suke da sabani a kansu, domin samun damar yin aiki tare a dukkanin bangarori, wanda hakan zai amfanar da al’ummomin kasashen biyu da kuma yankin baki daya.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, babban abin da Iran din take bukata hakan ya zama a aikace, ba kawai a kalamai na fatar baki ba.

A wata hira da ya yi da tashar kasar Saudiyya a ranar 27 ga watan Afirilun da ya gabata, yariman Saudiyya mai jiran gado Muhammad Bin Salman, ya bayyana cewa suna son kulla kyakkyawar alaka da Iran, kasantuwarta kasa makwabciya ga Saudiyya, duk da cewa akwai wasu matsaloli da suke hana hakan, amma dai suna yin aiki tare da kawayensu domin warware wadannan matsaloli.

A cikin jawabin da jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar a jiya Lahadi ya yi ishara da cewa, akwai shugabannin kasashen larabawa da suke da niyar ziyartar Iran, amma Amurka ce take hana su, tare da nisantar da su daga kulla duk wata alaka da kasar ta Iran.

342/