ABNA24 : Kawo lokacin dai an cimma matsaya kan dage wa Iran, takunkumi a wasu bangarori.
Baya ga haka Iran, na mai bukatar a dage mata takunkumi a bangaren makamashi, kere kere motoci, inshore da kuma tashohin jiragen ruwa, da kuma wasu daidaikun mutane da hukumomi.
Karamin ministan harkokin waje, kana mai jagorantar tawagar Iran a tattauanwar, Abbas Araghchi, ya ce an shiga wani mataki na rubata ababen da aka cimma a yarjejeniyar.
Ya ce an kai wani mataki inda aka samu daidaito a bangarori daban daban, an samu daidaito a wasu fanonin kamar yadda ke akwai sabani, a wasu bangarorin inji shi.
Sabani game da batun bukiliya da kuma takunkumai su ne dai ake da sabani a game da su.
Ya kuma ce duk akwai ci gaba a tattaunawar amma ba za’a bayyana cewa ba ga takamaimai lokacin da zamu cimma yarjejeniya, saboda ko wane bangare yana da shi bukatu.
342/