ABNA24 : Matakin kungiyar ta FACT ya biyo bayan da bangarori daban daban a yankin suka isa a kasar ta Chadi, inda suka bukaci haya teburin tattaunawa domin warware rikicin kasar bayan mutuwar ba zata ta shugaba Idriss Deby Itno.
Dama dai ‘yan tawayen kasar sun tsagaita wuta a wani mataki da suka ce na bada dama ne domin gudanar da jana’izar Idriss Deby.
Kakakin ‘yan tawayen mau saudake da makamai, Mahamat Mahadi Ali, ya ce sun amince tsagaita wuta, domin samun mafita ta siyasa game da matsalolin kasar ta Chadi, kuma wannan dama shi ne babban fatanmu tun ba shekaru biyar da suka gabata, na cewa hawa teburin tattaunawa shi ne mafita game da rikicin Chadi, inji shi.
A halin da ake ciki dai an kasashen kungiyar G5 Sahel da faransa, sun wakilta shugabannin kasasehn jamhuriyar Nijar da kuma na Mauritania, domin shiga tsakani a rikicin kasar ta Chadi, kuma tuni suka tattauna da wasu bangarorin siyasa na kasar ta Chadi.
342/