ABNA24 : A lokacin da yake gabatar da jawabi a jiya a wurin janazar tsohon shugaban kasar Chadi Idriss Deby a birnin Njamena, Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa, Faransa ba za ta taba zura ido a kan duk wata barazana a kan kaar Chadi ba, daga cikin kasar ne ko daga wajenta.
Haka nan kuam macron ya bayyana juyayinsa dangane da kisan Idriss Deby, wanda ya bayyana shi a matsayin amini kuma abokin aiki ga gwamnatin kasar Faransa, inda ya ce Faransa za ta ci gaba da yin aiki tare da kasar Chadi a dukkanin bangarori.
A jiya ne dai aka gudanar da janazar tsohon shugaban kasar ta Chadi Idriss Deby, wanda ya mutu a ranar Talata da ta gabata, biyo bayan raunukan da ya samu a lokacin da ake fafatawa da ‘yan tawaye.
Idriss Deby, wanda ya kasance yana dasawa da turwan yamma musamman kasar Faransa, ya kwashe tsawon shekaru 30 yana mulki a kasar Chadi, biyo bayan wani juyin mulki da ya jagoranta a kasar tare da taimakon Faransa.
Yanzu haka dai majalisar mulki ta sojoji da aka kafa karkashin shugabancin dan Idris Deby Muhammad Idriss Deby ce take tafiyar da sha’anin mulki a kasar, duk da cewa wasu bayanai na nuni da cewa, wasu manyan jami’an sojin kasar ba su gamsu da hakan ba.
342/