19 Afirilu 2021 - 14:40
Visar Ghana Na A Matsayin Ta 77 Wajen Aminci A Duniya

Cibiyar nan ta “Henley and Partners” wacce take sanya idanu akan kai da komowar mutane ta hanyar amfani da takardun shiga da fice tun a 2006, ta kuma bayyana cewa; masu dauke da Passport din na kasar Ghana za su iya shiga kasashe 65 a duniya ba tare da izinin shiga na (visa) ba.

Wasu daga cikin kasashen sun kunshi; New Zealand, Hadaddiyar Daular Larabawa, Finland, sai kuma Singapore, Guyana da Tanzania.

A shekarar 2000 pasport din kasar ta Ghana yana a matsayi na 75 ne a duniya.

Ita kuwa kasar Nigeria, takardun shiga da ficenta na Passport yana a matsayin na 95 ne kuma masu dauke da shi za su iya samun shiga kasashe 46 ba tare da Visa ba.

Kasar Japan ce dai ta daya a duniya wajen darajar passport , ta yadda masu dauke da shi za su iya shiga kasashe 193 ba tare da sun sami izini na Visa ba.

342/