15 Afirilu 2021 - 14:20
Jamhuriyar Nijar Ta Karbi Rigakafin Korona Na Tsarin COVAX

Gwamnatin jamhuriyar Nijar, ta karbi riga kafin cutar korona na cikin tsarin nan na COVAX, dake samun goyan bayan kungiyar tarayyar turai.

ABNA24 : Firaministan kasar ne Malam Ouhoumou Mahammadou, ya karbi rigakafin da ya kunshi kwalba dubu 350.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Nijar ta karbi riga kafin korona bayan wanda ta karba a matsayin tallafi daga kasar China a kwanan baya.

Alkalumman baya baya nan dai a Nijar, sun nuna cewa mutum 5,108 suka kamu da cutar a fadin kasar, sai kuma 190 da suka rasa rayukansu sanadin cutar, yayin da 4,764 suka warke.

A ranar Talatar data gabata mutum 27 ne suka kamu a fadin kasar sai kuma guda da ya rasa ransa.

Nijar dai ba ta daga cikin kasashen da cutar ta yi wa mummunan illah, amma duk da hakan hukumomin kasar na kira ga jama’a da su kiyaye matakan yaki da annobar.

342/