11 Afirilu 2021 - 17:21
‘Yan Benin Na Kada Kuri'a A Zaben Shugaban Kasa

Al’ummar jamhuriyar Benin, na kada kuri’a a zaben shugaban kasar a wannan Lahadin.

ABNA24 : Shugaba Patrice Talon mai neman wa’adi na biyu, zai fafata ne da manyan masu hamayya da shi guda biyu a zaben wato Alassane Soumanou da Corentin Kohoue.

Saidai yawancin shugabannin ‘yan adawa sun fice daga kasar bayan da kotu ta haramta masu shiga zaben.

Ana kada kuri’a ne bayan kammala yakin neman zaben, da aka kwashe kwanaki ana rikici a yankunan tsakiya da arewacin kasar.

Hukumar zaben kasar ta ce ba a samu kai kayan zabe ba a yankin arewacin kasar bayan da masu zanga-zanga suka toshe hanya yayin da ya rage kwana daya a je zaben.

Kafin hakan dai babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci kasashen Chadi da Benin su mutunta yancin jama’a da kuma fadin albarkacin baki yayin da kasashen biyu ke zabe a wannan Lahadin.

342/